Zab 2:5-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ya yi musu magana da fushi,Ya razanar da su da hasalarsa,

6. Ya ce, “A bisa Sihiyona, dutsena tsattsarka,Na naɗa sarkina.”

7. Sarkin ya ce, “Zan yi shelar abin da Ubangiji ya hurta.Ubangiji ya ce mini, ‘Kai ɗana ne,Yau ne na zama mahaifinka.

8. Ka yi roƙo, zan kuwa ba ka dukan al'ummai,Dukan duniya kuma za ta zama taka.

9. Za ka mallake su da sandan ƙarfe,Za ka farfashe su kamar tukunyar yumɓu.’ ”

10. Yanzu ku kasa kunne gare ni, ku sarakuna,Ku mai da hankali, ku mahukunta!

Zab 2