Zab 15:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wane ne zai iya zama cikin Haikalinka?Wa zai iya tsayawa a Sihiyona, wato tudunka tsattsarka?

2. Sai dai mutumin da yake biyayya ga Allah da kowane abu,Yana kuwa aikata abin da yake daidai,Wanda yake faɗar gaskiya da zuciya ɗaya,

3. Wanda kuma ba ya ɓāta sunan waɗansu.Ba ya zargin abokansa,Ba ya kuwa baza jita-jita a kan maƙwabtansa.

4. Yakan raina waɗanda Allah ya ƙi su,Amma yana girmama waɗanda suke yi wa Ubangiji biyayya,Kullum yana cika alkawaran da ya yi ko ta halin ƙaƙa,

Zab 15