Zab 149:2-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ki yi murna, ke Isra'ila, sabili da Mahaliccinki,Ku yi farin ciki, ku jama'ar Sihiyona, sabili da Sarkinku!

3. Ku yabi sunansa, kuna taka rawa,Ku kaɗa bandiri da garayu, kuna yabonsa.

4. Ubangiji yana jin daɗin jama'arsa,Yakan girmama mai tawali'u ya sa ya ci nasara.

5. Bari jama'ar Allah su yi farin ciki saboda cin nasararsu,Su raira waƙa don farin ciki.

6. Bari su yi sowa da ƙarfiSa'ad da suke yabon Allah, da takubansu masu kaifi.

7. Don su ci nasara bisa al'ummai,Su kuma hukunta wa jama'a,

Zab 149