Zab 139:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, ka jarraba ni, ka san ni.

2. Ka sa dukan abin da nake yi,Tun daga can nesa ka gane dukan tunanina.

3. Kana ganina, ko ina aiki, ko ina hutawa,Ka san dukan ayyukana.

4. Tun kafin in yi maganaKa riga ka san abin da zan faɗa.

Zab 139