Zab 127:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Idan ba Ubangiji ne ya gina gidan ba,Aikin magina banza ne.Idan ba Ubangiji ne ya tsare birnin ba,Ba wani amfani a sa matsara su yi tsaro.

2. Ba wani amfani a sha wahalar aiki saboda abinci,A yi asubancin tashi, a yi makarar kwanciya,Gama Ubangiji yakan hutar da waɗanda yake ƙauna.

Zab 127