Zab 127 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Yabon Alherin Ubangiji

1. Idan ba Ubangiji ne ya gina gidan ba,Aikin magina banza ne.Idan ba Ubangiji ne ya tsare birnin ba,Ba wani amfani a sa matsara su yi tsaro.

2. Ba wani amfani a sha wahalar aiki saboda abinci,A yi asubancin tashi, a yi makarar kwanciya,Gama Ubangiji yakan hutar da waɗanda yake ƙauna.

3. 'Ya'ya kyauta ne daga wurin Ubangiji,Albarka ce ta musamman.

4. 'Ya'ya maza da mutum ya haifa a lokacin ƙuruciyarsaKamar kibau suke a hannun mayaƙi.

5. Mai farin ciki ne mutumin da yake da irin waɗannan kibau da yawa!Faufau ba za a ci nasara a kansa ba,Sa'ad da ya kara da maƙiyansa a wurin shari'a.