Zab 125:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waɗanda suke dogara ga Ubangiji,Suna kama da Dutsen Sihiyona,Wanda ba zai jijjigu ba, faufau.Faufau kuma ba za a kawar da shi ba.

2. Kamar yadda duwatsu suka kewaye Urushalima,Haka nan Ubangiji zai kewaye jama'arsa,Daga yanzu har abada.

3. Ba a koyaushe mugaye za su yi mulki a ƙasar jama'ar Allah ba,Idan kuwa suka yi, to, ya yiwu jama'ar Allah su yi laifi.

Zab 125