1. Na dogara ga Ubangiji domin zaman lafiya,Wauta ce idan kun ce mini,“Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu,
2. Domin mugaye sun ja bakkunansu,Sun kuma ɗana kibansuDomin su harbi mutanen kirki a duhu.
3. Ba abin da mutumin kirki zai iya yiSa'ad da kome ya lalace.”
4. Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa,Yana da kursiyinsa a Sama.Yana kallon dukan mutaneYana sane da abin da suke yi.