1. Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar girmansa,Ku sanar wa sauran al'umma abubuwan da ya yi!
2. Ku raira masa waƙa, ku raira yabo gare shi,Ku faɗi dukan abubuwa masu banmamaki da ya yi!
3. Ku yi murna saboda mu nasa ne,Ku yi murna dukanku da kuke bauta wa Ubangiji!
4. Ku je wurin Ubangiji neman taimako,Ku tsaya a gabansa koyaushe.
5-6. Ya ku zuriyar bawansa Ibrahim,Ya ku zuriyar zaɓaɓɓensa Yakubu,Ku tuna da mu'ujizansa masu girma, masu banmamaki,Ku tuna kuma da hukuntai waɗanda ya yanke.
7. Shi Ubangiji, shi ne Allahnmu,Umarnansa domin dukan duniya ne.