Zab 101:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Waƙata ta aminci ce da gaskiya.Ina raira maka ita, ya Ubangiji.

2. Abin da nake yi ba zai zama laifi ba,Yaushe za ka zo wurina?Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana.

3. Ba zan jure da mugunta ba ko kaɗan.Na ƙi jinin ayyukan waɗanda suka bijire wa Allah,Ba ruwana da su.

Zab 101