1. Ya Ubangiji, me ya sa kake can nesa?Me ya sa ka ɓoye kanka a lokacin wahala?
2. Mugaye suna fāriya, suna kuma tsananta wa matalauta,Ɗana tarkon da suka yi yă kama su.
3. Mugun mutum yana fāriya da mugayen manufofinsa,Mai haɗama yakan zagi Ubangiji ya kuma ƙi shi.
4. Mugun mutum da girmankansa yana cewa, “Ba Allah!”Wannan ne abin da mugu yake tunani.