1. Ya ku mutanen Isra'ila, ku ji maganar Ubangiji,Gama Ubangiji yana da shari'a da ku, ku mazaunan ƙasar.“Gama ba gaskiya, ko ƙauna,Ko sanin Ubangiji a ƙasar.
2. Akwai rantsuwa, da ƙarya, da kisankai, da sata, da zina,Da kama-karya, da zub da jini a kai a kai.
3. Saboda haka ƙasar za ta yi makoki,Dukan waɗanda yake zaune a cikinta za su yi yaushi.Namomin jeji kuma, da tsuntsaye, da kifaye za su ƙare.