13. Naƙudar haihuwarsa ta zo,Amma shi wawan yaro ne,Bai fito daga mahaifar ba.
14. Zan fanshe su daga ikon lahira.Zan fanshe su daga mutuwa.Ya mutuwa, ina annobanki?Ya kabari, ina halakarka?Kan kawar da juyayi daga wurina.
15. Ko da yake Isra'ila tana bunƙasa kamar ciyayi,Iskar gabas, wato iskar da za ta zo daga jeji,Za ta busar da maɓuɓɓugarsu da idon ruwansu,Za ta lalatar da abubuwa masu amfani da yake cikin taskarsu.