Yush 12:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. A cikin mahaifa kakansu Yakubu ya kama diddigen ɗan'uwansa,Sa'ad da ya zama baligi ya yi kokawa da Allah.

4. Ya yi kokawa da mala'ika ya yi rinjaye.Ya yi kuka, ya roƙi albarka.Ya sadu da Allah a Betel,A can Allah ya yi magana da shi.

5. Ubangiji Allah Mai Runduna,Sunansa Ubangiji,

6. Sai ku koma wurin Allahnku,Ku yi alheri, ku yi adalci,Ku saurari Allahnku kullayaumin.

7. Ubangiji ya ce, “Ɗan kasuwa wanda yake da ma'aunin algus a hannunsa.Yana jin daɗin yin zalunci.

8. Mutanen Ifraimu sun ce, ‘Hakika, mun zama attajirai,Mun samar wa kanmu dukiya.A cikin harkokinmu ba za a sami wata mugunta ba.’

Yush 12