Yah 7:20-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

20. Taron suka amsa suka ce, “Kana da iska! Wa yake neman kashe ka?”

21. Yesu ya amsa musu ya ce, “Aiki ɗaya kawai na yi, dukanku kuwa kuna mamakinsa.

22. Musa ya bar muku kaciya, (ba ko shi ya fara ba, tun kakannin kakanni ne), ga shi kuma, kukan yi wa mutum kaciya ko a ran Asabar ma.

23. To, in ana yi wa mutum kaciya ran Asabar don gudun keta Shari'ar Musa, kwa yi fushi don na warkar da mutum sarai ran Asabar?

24. Kada ku yi hukunci da zato, amma ku yi hukunci da adalci.”

25. Sai waɗansu mutanen Urushalima suka ce, “Ashe, ba wannan ne mutumin da suke nema su kashe ba?

26. Ga shi nan kuwa, yana magana a fili, ba su ce masa kome ba! Ya yiwu kuma shugabanni sun san lalle wannan shi ne Almasihu?

27. Wannan kam, mun san daga inda yake, amma sa'ad da Almasihu ya zo ba wanda zai san daga inda yake.”

28. Yesu yana koyarwa a Haikalin ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “Kun dai san ni, kun kuma san daga inda nake. Ban fa zo domin kaina ba. Wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, shi kuwa ba ku san shi ba.

29. Ni na san shi, domin daga wurinsa na fito, shi ne kuwa ya aiko ni.”

30. Don haka suka nema su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna.

31. Duk da haka mutane da yawa cikin taron sun gaskata da shi, suna cewa, “Sa'ad da Almasihu ya zo, zai yi mu'ujizai fiye da na mutumin nan?”

32. Farisiyawa suka ji taro suna raɗeraɗinsa haka, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki dogaran Haikali su kamo shi.

Yah 7