1. Bayan haka Yesu ya haye Tekun Galili, wato Tekun Tibariya.
2. Sai taro mai yawa suka bi shi, don sun ga mu'ujizan da yake yi ga marasa lafiya.
3. Sai Yesu ya hau dutse ya zauna a can tare da almajiransa.
4. To, Idin Ƙetarewa, wato idin Yahudawa, ya gabato.
5. Da Yesu ya ɗaga kai ya hango babban taro yana doso shi, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayo gurasar da mutanen nan za su ci?”
6. Ya faɗi haka ne fa domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi.
7. Filibus ya amsa ya ce, “Ai, ko gurasar dinari metan ma ba ta isa ko wannensu ya sami kaɗan ba.”
8. Sai Andarawas ɗan'uwan Bitrus ɗaya daga cikin almajiransa, ya ce masa,
9. “Ga wani ɗan yaro nan da gurasa biyar na sha'ir, da kuma kifi biyu. Amma me waɗannan za su yi wa mutane masu yawa haka?”
10. Yesu ya ce, “Ku ce wa mutane su zauna.” Wuri ne kuwa mai ciyawa. Sai mazaje suka zazzaune, su wajen dubu biyar.