Yah 19:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'an nan Bilatus ya sa a tafi da Yesu, a yi masa bulala.

2. Sai soja suka yi wani kambi na ƙaya suka sa masa a kā, suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura.

3. Suka yi ta zuwa wurinsa, suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” suna ta marinsa.

4. Sai Bilatus ya sāke fitowa, ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi, domin ku san ban same shi da wani laifi ba.”

5. Sa'an nan Yesu ya fito, sāye da kambin ƙayar, da alkyabba mai ruwan jar garura. Sai Bilatus ya ce musu, “To, ga mutumin!”

6. Da manyan firistoci da dogaran Haikali suka gan shi, suka ɗau kururuwa suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi ku da kanku, ku gicciye shi, ni kam, ban same shi da wani laifi ba.”

Yah 19