Yah 19:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'an nan Bilatus ya sa a tafi da Yesu, a yi masa bulala.

2. Sai soja suka yi wani kambi na ƙaya suka sa masa a kā, suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura.

3. Suka yi ta zuwa wurinsa, suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” suna ta marinsa.

Yah 19