Yah 18:38-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Bilatus ya ce masa, “Wane abu ne, wai shi gaskiya?”Bayan da ya faɗi haka, ya sāke fitowa wurin Yahudawa, ya ce musu, “Ni kam, ban same shi da wani laifi ba.

39. Amma dai kuna da wata al'ada, in Idin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku mutum ɗaya. To, kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?”

40. Sai suka sāke ɗaukar kururuwa suna cewa, “A'a, ba wannan ba, sai dai Barabbas!” Barabbas ɗin nan kuwa ɗan fashi ne.

Yah 18