32. Wannan kuwa don a cika maganar da Yesu ya yi ne, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi.
33. Sai Bilatus ya koma cikin fāda, ya kira Yesu ya ce masa, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?”
34. Yesu ya amsa ya ce, “Wato wannan faɗarka ce, ko kuwa waɗansu ne suka ce da ni haka a wurinka?”
35. Bilatus ya amsa ya ce, “Ni Bayahude ne? Ai, jama'arku da manyan firistoci su ne suka bāshe ka gare ni. Me ka yi?”