Yah 17:13-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Amma yanzu ina zuwa wurinka. Ina faɗar wannan magana tun ina duniya, domin farin cikina ya zama cikakke a zukatansu.

14. Na faɗa musu maganarka, duniya kuwa ta ƙi su, domin su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.

15. Ba na roƙonka ka ɗauke su daga duniya, sai dai ka kāre su daga Mugun nan.

16. Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.

17. Ka tsarkake su cikin gaskiya. Maganarka ita ce gaskiya.

18. Kamar yadda ka aiko ni duniya, haka ni ma na aike su duniya.

19. Saboda su ne nake miƙa kaina, domin su ma a tsarkake su cikin gaskiya.

20. “Ba kuwa waɗannan kaɗai nake roƙa wa ba, har ma masu gaskatawa da ni ta maganarsu,

21. domin dukansu su zama ɗaya, kamar yadda kai, ya Uba, kake cikina, ni kuma nake cikinka, haka su ma su kasance cikinmu, domin duniya ta gaskata, cewa kai ne ka aiko ni.

22. Ɗaukakar da ka yi mini, ita na yi musu, domin su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya,

23. ni a cikinsu, kai kuma a cikina, domin su zama ɗaya sosai, duniya ta gane kai ne ka aiko ni, ta kuma gane ka ƙaunace su kamar yadda ka kaunace ni.

24. Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, domin ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba.

Yah 17