Yah 16:32-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. To, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansu, ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka kuwa ba ni kaɗai nake ba, domin Uba na tare da ni.

33. Na faɗa muku wannan ne domin a gare ni ku sami salama. A duniya kuna shan wuya, amma dai ku yi farin ciki, ai, na yi nasara da duniya.”

Yah 16