Yah 13:24-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Sai Bitrus ya alamta masa ya ce, “Gaya mana, da wa yake?”

25. Shi kuwa da yake kishingiɗe haka gab da Yesu ya karkata, ya ce masa, “Ya Ubangiji, wane ne?”

26. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan tsoma 'yar lomar nan in ba shi.” Da ya tsoma 'yar lomar kuwa, sai ya ba Yahuza, Ɗan Saminu Iskariyoti.

Yah 13