Yah 11:55-57 Littafi Mai Tsarki (HAU)

55. Ana nan, Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya gabato, mutane da yawa daga ƙauye suka tafi Urushalima su tsarkake kansa kafin idin.

56. Suka yi ta neman Yesu, suna tsaitsaye a Haikali, suna ce wa juna, “Me kuka gani? Zai zo idin kuwa?”

57. Don dā ma, manyan firistoci da Farisiyawa sun yi umarni, cewa kowa ya san inda Yesu yake, ya zo ya faɗa, su kama shi.

Yah 11