Yah 11:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wani mutum ne ya yi rashin lafiya, sunansa Li'azaru na Betanya, ƙauyen su Maryamu da 'yar'uwarta Marta.

2. Maryamun nan kuwa, wadda ɗan'uwanta Li'azaru ba shi da lafiya, ita ce wadda ta shafa wa Ubangiji man ƙanshi, ta kuma shafe ƙafafunsa da gashinta.

Yah 11