W. Yah 7:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan wannan na ga mala'iku huɗu, a tsaye a kusurwa huɗu ta duniya, suna tsare da iskokin nan huɗu na duniya, don kada wata iska ta busa a kan ƙasa, ko a kan teku, ko a kan wani itace.

2. Sai na ga wani mala'ika yana hawa daga mafitar rana, riƙe da hatimin Allah Rayayye. Sai ya yi wa mala'ikun nan huɗu magana da murya mai ƙarfi, waɗanda aka bai wa ikon azabtar da ƙasa da teku,

3. yana cewa, “Kada ku azabtar da ƙasa, ko teku, ko itatuwa, sai mun buga wa bayin Allahnmu hatimi a goshinsu tukuna.”

W. Yah 7