1. To, ina gani sa'ad da Ɗan Ragon nan ya ɓamɓare ɗaya daga cikin hatiman nan bakwai, na ji ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan huɗu ta yi magana kamar aradu ta ce, “Zo.”
2. Da na duba, ga farin doki, mahayinsa kuma yana da baka, aka ba shi kambi, ya kuwa fita yana mai nasara, domin ya ƙara cin nasara.
3. Da ya ɓamɓare hatimi na biyu, na ji rayayyiyar halittar nan ta biyu ta ce, “Zo.”
4. Sai wani jan doki ya fito, aka kuma ba mahayinsa izini yă ɗauke salama daga duniya, don mutane su kashe juna, aka kuma ba shi babban takobi.
5. Da ya ɓamɓare hatimi na uku, na ji rayayyiyar halittar nan ta uku ta ce, “Zo.” Da na duba, ga baƙin doki, mahayinsa kuwa da mizani a hannunsa.
6. Sai na ji kamar wata murya a tsakiyar rayayyun halittar nan huɗu tana cewa, “Mudun alkama dinari guda, mudu uku na sha'ir dinari guda, sai dai kada ka ɓāta mai da kuma ruwan inabi!”
7. Da ya ɓamɓare hatimi na huɗu, na ji muryar rayayyiyar halittan nan ta huɗu ta ce, “Zo.”