1. To, ina gani sa'ad da Ɗan Ragon nan ya ɓamɓare ɗaya daga cikin hatiman nan bakwai, na ji ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan huɗu ta yi magana kamar aradu ta ce, “Zo.”
2. Da na duba, ga farin doki, mahayinsa kuma yana da baka, aka ba shi kambi, ya kuwa fita yana mai nasara, domin ya ƙara cin nasara.
3. Da ya ɓamɓare hatimi na biyu, na ji rayayyiyar halittar nan ta biyu ta ce, “Zo.”