3. Sai suka sāke yin sowa, suna cewa,“Halleluya! Hayaƙinta yana tashi har abada abadin.”
4. Sai dattawan nan ashirin da huɗu, da rayayyun halittan nan huɗu, suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, shi da yake zaune a kan kursiyin, suna cewa, “Amin. Halleluya!”
5. Sai aka ji wata murya daga kursiyin, tana cewa,“Ku yabi Allahnmu, ya ku bayinsa,Ku da kuke jin tsoronsa, yaro da babba.”
6. Sai na ji kamar wata sowar ƙasaitaccen taro, kamar ƙugin ruwa mai gudu, kamar aradu mai ƙara, suna cewa,“Halleluya! Gama Ubangiji AllahnmuMaɗaukaki shi ne yake mulki.