1. Bayan wannan na ji kamar wata sowa mai ƙarfi ta ƙasaitaccen taro a Sama, suna cewa,“Halleluya! Yin ceto, da ɗaukaka, da iko, sun tabbata ga Allahnmu,
2. Don hukuncinsa daidai yake, na adalci ne,Ya hukunta babbar karuwar nan wadda ta ɓata duniya da fasikancinta,Ya kuma ɗauki fansar jinin bayinsa a kanta.”
3. Sai suka sāke yin sowa, suna cewa,“Halleluya! Hayaƙinta yana tashi har abada abadin.”
4. Sai dattawan nan ashirin da huɗu, da rayayyun halittan nan huɗu, suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, shi da yake zaune a kan kursiyin, suna cewa, “Amin. Halleluya!”
5. Sai aka ji wata murya daga kursiyin, tana cewa,“Ku yabi Allahnmu, ya ku bayinsa,Ku da kuke jin tsoronsa, yaro da babba.”
6. Sai na ji kamar wata sowar ƙasaitaccen taro, kamar ƙugin ruwa mai gudu, kamar aradu mai ƙara, suna cewa,“Halleluya! Gama Ubangiji AllahnmuMaɗaukaki shi ne yake mulki.
7. Mu yi ta murna da farin ciki matuƙa,Mu kuma ɗaukaka shi,Domin bikin Ɗan Ragon nan ya zo,Amaryarsa kuma ta kintsa.
8. An yardar mata ta sa tufafin lallausan lilinmai ɗaukar ido, mai tsabta.”Lallausan lilin ɗin nan, shi ne aikin adalci na tsarkaka.
9. Sai mala'ikan ya ce mini, “Rubuta wannan, ‘Albarka tā tabbata ga waɗanda aka gayyata, zuwa cin abincin bikin Ɗan Ragon nan.’ ” Ya kuma ce mini, “Wannan ita ce Maganar Allah ta gaskiya.”