W. Yah 17:4-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Matar kuwa tana saye da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma ja wur, ta ci ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u, tana a riƙe da ƙoƙon zinariya a hannunta, cike da abubuwan ƙyama, da ƙazantar fasikancinta.

5. A goshinta kuma an rubuta wani sunan asiri, “Babila mai girma, uwar karuwai, uwar abubuwa masu banƙyama na duniya.”

6. Sai na ga matar ta bugu da jinin tsarkaka, da kuma jinin mashaidan Yesu.Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai da gaske.

7. Amma mala'ikan ya ce mini, “Don me kake mamaki? Zan buɗa maka asirin matar nan, da kuma na dabbar nan mai kawuna bakwai, da ƙaho goma, da take ɗauke da ita.

8. Dabbar nan da ka gani, wadda dā take nan, a yanzu kuwa ba ta, za ta hawo ne daga ramin mahallaka, ta je ta hallaka, mazaunan duniya kuma waɗanda tun a farkon duniya, ba a rubuta sunayensu a Littafin Rai ba, za su yi mamakin ganin dabbar, don dā tana nan, a yanzu ba ta, za ta kuma dawo.

9. Fahimtar wannan abu kuwa, sai a game da hikima. Wato, kawuna bakwai ɗin nan tuddai ne guda bakwai, waɗanda matar take a zaune a kai.

W. Yah 17