W. Yah 17:2-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. wadda sarakunan duniya suka yi fasikanci da ita, wadda kuma mazaunan duniya suka jarabtu da yin fasikanci da ita.”

3. Sai ya ɗauke ni ya tafi da ni zuwa jeji, Ruhu yana iza ni, sai na ga wata mace a kan wata dabba ja wur, duk jikin dabbar sunayen saɓo ne, tana kuma da kawuna bakwai, da ƙaho goma.

4. Matar kuwa tana saye da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma ja wur, ta ci ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u, tana a riƙe da ƙoƙon zinariya a hannunta, cike da abubuwan ƙyama, da ƙazantar fasikancinta.

5. A goshinta kuma an rubuta wani sunan asiri, “Babila mai girma, uwar karuwai, uwar abubuwa masu banƙyama na duniya.”

6. Sai na ga matar ta bugu da jinin tsarkaka, da kuma jinin mashaidan Yesu.Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai da gaske.

7. Amma mala'ikan ya ce mini, “Don me kake mamaki? Zan buɗa maka asirin matar nan, da kuma na dabbar nan mai kawuna bakwai, da ƙaho goma, da take ɗauke da ita.

8. Dabbar nan da ka gani, wadda dā take nan, a yanzu kuwa ba ta, za ta hawo ne daga ramin mahallaka, ta je ta hallaka, mazaunan duniya kuma waɗanda tun a farkon duniya, ba a rubuta sunayensu a Littafin Rai ba, za su yi mamakin ganin dabbar, don dā tana nan, a yanzu ba ta, za ta kuma dawo.

9. Fahimtar wannan abu kuwa, sai a game da hikima. Wato, kawuna bakwai ɗin nan tuddai ne guda bakwai, waɗanda matar take a zaune a kai.

10. Har wa yau kuma, sarakuna ne guda bakwai, waɗanda biyar daga cikinsu aka tuɓe, ɗaya yana nan, ɗayan bai zo ba tukuna, sa'ad da ya zo kuwa, lalle zamaninsa na lokaci kaɗan ne kawai.

W. Yah 17