W. Yah 16:8-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sai mala'ika na huɗu ya juye abin da yake a tasarsa a rana, sai aka yardar mata ta ƙona mutane da wuta.

9. Sai matsanancin zafi ya ƙona mutane, har suka zagi sunan Allah, shi da yake da ikon waɗannan bala'i, ba su kuwa tuba sun ɗaukaka shi ba.

10. Mala'ika na biyar ya juye abin da yake a tasarsa a kursiyin dabbar nan, sai mulkinta ya zama duhu, har mutane suka ciji leɓunansu don azaba,

11. suka zagi Allah Mai Sama saboda azabarsu da miyakunsu, ba su kuma tuba da ayyukansu ba.

12. Mala'ika na shida ya juye abin da yake a tasarsa a babban kogin nan Yufiretis, sai ruwansa ya ƙafe, don a shirya wa sarakuna daga gabas tafarki.

13. Na kuma ga baƙaƙen aljannu masu kama da kwaɗi gudu uku, suna fitowa daga bakin macijin nan, da bakin dabbar nan, da kuma bakin annabin nan na ƙarya,

14. su iskoki ne, aljannu masu yin abubuwan al'ajabi, masu zuwa wurin sarakunan duniya duka, don su tara su saboda yaƙi a babbar ranar nan ta Allah Maɗaukaki.

15. (“Ga ni nan a tafe kamar ɓarawo! Albarka tā tabbata ga wanda yake a zaune a faɗake, yana saye da tufafinsa, don kada ya tafi tsirara, a ga tsiraicinsa.”)

16. Sai suka tattara su a wurin da ake kira Armageddon da Yahudanci.

17. Mala'ika na bakwai ya juye abin da yake a tasarsa a sararin sama, sai aka ji wata murya mai ƙara daga Haikali, wato, daga kursiyin, ta ce, “An gama!”

W. Yah 16