W. Yah 16:2-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Daga nan mala'ikan farko ya je ya juye abin da yake a tasarsa a kan duniya, sai kuwa waɗansu mugayen miyaku masu azabtarwa suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar nan, suke kuma yi wa siffarta sujada.

3. Mala'ika na biyu ya juye abin da yake a tasarsa a teku, ya zama kamar jinin mataccen mutum, kowane abu mai rai na cikin teku kuma ya mutu.

4. Mala'ika na uku ya juye abin da yake a tasarsa a koguna da maɓuɓɓugan ruwa, sai suka zama jini.

5. Na kuwa ji mala'ikan ruwa yana cewa,“Kai mai adalci ne a hukuncin nan naka,Ya kai Mai Tsarki, wanda kake a yanzu, kake kuma a dā.

6. Don mutane sun zub da jinin tsarkaka da na annabawa,Ga shi kuwa, ka ba su jini su sha.Sakamakonsu ke nan!”

7. Sai na ji wata murya a bagadin ƙona turare, tana cewa,“Hakika, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki,Hukuncinka daidai yake, na adalci ne kuma!”

8. Sai mala'ika na huɗu ya juye abin da yake a tasarsa a rana, sai aka yardar mata ta ƙona mutane da wuta.

9. Sai matsanancin zafi ya ƙona mutane, har suka zagi sunan Allah, shi da yake da ikon waɗannan bala'i, ba su kuwa tuba sun ɗaukaka shi ba.

10. Mala'ika na biyar ya juye abin da yake a tasarsa a kursiyin dabbar nan, sai mulkinta ya zama duhu, har mutane suka ciji leɓunansu don azaba,

11. suka zagi Allah Mai Sama saboda azabarsu da miyakunsu, ba su kuma tuba da ayyukansu ba.

12. Mala'ika na shida ya juye abin da yake a tasarsa a babban kogin nan Yufiretis, sai ruwansa ya ƙafe, don a shirya wa sarakuna daga gabas tafarki.

W. Yah 16