W. Yah 15:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na kuma ga wata alama a Sama, mai girma, mai banmamaki, mala'iku bakwai masu bala'i bakwai, waɗanda suke bala'in ƙarshe, don su ne iyakacin fushin Allah.

2. Sai na ga wani abu kamar bahar na gilas, gauraye da wuta, na kuma ga waɗanda suka yi nasara da dabbar nan, da siffarta, da kuma lambar sunanta, a tsaitsaye a bakin bahar na gilas, da molayen yabon Allah a hannunsu.

3. Suna raira waƙar da Musa bawan Allah ya yi, da kuma wadda ake yi wa Ɗan Ragon nan, suna cewa,“Ayyukanka manya ne, masu banmamaki,Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki!Hanyoyinka na adalci ne, na gaskiya ne kuma,Ya Sarkin al'ummai.

4. Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji,Ya kuma ɗaukaka sunanka?Domin kai kaɗai ne Mai Tsarki.Dukkan al'ummai za su zo su yi maka sujada,Don ayyukanka na adalci sun bayyana.”

5. Bayan wannan na duba, ga Wuri Mafi Tsarki a buɗe a Haikali a Sama.

W. Yah 15