6. Suna da ikon hana ruwan sama, don kada a yi ruwa a duk kwanakin da suke yin annabci, suna kuma da iko a kan ruwa, su mai da shi jini, su kuma ɗora wa duniya kowane irin bala'i, a duk lokacin da suke so.
7. Bayan da suka ƙare shaidarsu, sai wata dabba mai fitowa daga mahallaka tă yaƙe su, ta cinye su, ta kashe su,
8. a kuma bar gawawwakinsu a kan hanyar babban birnin nan da ake kira Saduma da Masar ga ma'ana ta ruhu, a inda aka gicciye Ubangijinsu.
9. Mutanen dukkan jama'a, da kabila, da harshe, da al'umma za su riƙa kallon gawawwakinsu, har kwana uku da rabi, su kuwa ƙi yarda a binne su.
10. Mazaunan duniya kuma, sai su yi ta alwashi a kansu, suna ta shagali, suna a'aika wa juna da kyauta, domin annabawan nan biyu dā sun azabtar da mazaunan duniya.
11. Amma bayan kwana uku da rabin nan, sai numfashin rai daga wurin Allah ya shiga a cikinsu, suka tashi a tsaye, matsanancin tsoro kuwa ya rufe waɗanda suka gan su.
12. Sai suka ji wata murya mai ƙara daga sama tana ce musu, “Ku hawo nan!” Sai suka tafi sama a cikin gajimare, maƙiyansu suna gani.