W. Yah 11:10-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Mazaunan duniya kuma, sai su yi ta alwashi a kansu, suna ta shagali, suna a'aika wa juna da kyauta, domin annabawan nan biyu dā sun azabtar da mazaunan duniya.

11. Amma bayan kwana uku da rabin nan, sai numfashin rai daga wurin Allah ya shiga a cikinsu, suka tashi a tsaye, matsanancin tsoro kuwa ya rufe waɗanda suka gan su.

12. Sai suka ji wata murya mai ƙara daga sama tana ce musu, “Ku hawo nan!” Sai suka tafi sama a cikin gajimare, maƙiyansu suna gani.

13. A nan tāke sai aka yi wata babbar rawar ƙasa, sai ushirin garin ya zube, mutum dubu bakwai aka kashe a rawar ƙasar, sauran kuwa suka tsorata, suka ɗaukaka Allah Mai Sama.

14. Bala'i na biyu ya wuce, ga kuma bala'i na uku yana zuwa nan da nan.

15. Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”

16. Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke a zaune a kan kursiyansu a gaban Allah suka fādi suka yi wa Allah sujada,

W. Yah 11