1. Sa'an nan aka ba ni wata gora kamar sanda, aka kuma ce mini, “Tashi ka auna Haikalin Allah, da bagadin hadaya, da kuma masu sujada a ciki,
2. amma kada ka auna harabar Haikalin, ka ƙyale ta, domin an ba da ita ga al'ummai, za su tattake tsattsarkan birnin nan har wata arba'in da biyu.
3. Zan kuma bai wa mashaidana biyu iko su yi annabci kwana dubu da metan da sittin, suna a saye da tsummoki.”
4. Waɗannan su ne itatuwan zaitun ɗin nan guda biyu, da fitilun nan biyu da suke a tsaye a gaban Ubangijin duniya.
5. In kuwa wani yana da niyyar cutarsu, sai wuta ta huro daga bakinsu, ta lashe maƙiyansu, duk mai niyyar cutarsu kuwa, ta haka ne lalle za a kashe shi.