7. Matsara masu kai da kawowa cikin birni suka same ni,Suka doke ni suka yi mini rauni.Matsaran da suke kan garu suka fige gyalena.
8. Ku yi mini alkawari ku matan Urushalima,Idan kun ga ƙaunataccena,Ku faɗa masa na yi suwu saboda ƙauna.
9. Ke mafi kyau cikin mata,Ki faɗi yadda ƙaunatacce naki yake.Wane abin sha'awa take gare shi,Har da za mu yi miki alkawari?
10. Ƙaunataccena kyakkyawa ne ƙaƙƙarfa kuma,Da ƙyar a sami ɗaya irinsa a cikin dubu goma.
11. Gashin kansa dogaye ne suna zarya,Baƙi wulik kamar jikin shaya.Kansa ya fi zinariya daraja.
12. Idanunsa kamar na kurciyoyi a bakin ƙorama,Waɗanda suka yi wanka da madara suna tsaye a bakin rafi.
13. Kumatunsa kyawawa ne kamar lambu,Wanda yake cike da tsire-tsire da kayan yaji.Leɓunansa kamar furen bi-rana ne, suna bulbulo da mur.