14. Hannuwansa kyawawa ne,Saye da ƙawanen da aka yi musu ado da duwatsu masu daraja.Ƙugu nasa sumul sumul ne kamar hauren giwa da aka manne da yakutu.
15. Cinyoyinsa kamar ginshiƙan da aka yi da dutsen alabasta,Aka kafa su a cikin kwasfar zinariya.Kamanninsa kamar Dutsen Lebanon ne,Da itatuwan al'ul ɗinsa mafi kyau.
16. Bakinsa yana da daɗin sumbata,Kome nasa yana faranta mini rai.Matan Urushalima, yadda ƙaunataccena yake ke nan.