Rut 4:2-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Bo'aza ya kuma kirawo goma daga cikin dattawan gari, ya ce musu, “Ku zauna nan.” Suka kuwa zauna.

3. Sa'an nan ya ce wa dangin nan nasa na kusa, “Ga Na'omi wadda ta komo daga ƙasar Mowab, tana so ta sayar da gonar Elimelek danginmu.

4. Don haka na ga ya kamata in sanar da kai cewa, ka saye ta a gaban waɗanda suke zaune a nan, da a gaban dattawan jama'a. Idan za ka fanshi gonar sai ka fanshe ta, idan kuwa ba za ka fansa ba, ka faɗa mini don in sani, gama daga kai sai ni muke da izinin fansar gonar.”Sai mutumin ya ce, “Zan fanshe ta.”

5. Sa'an nan Bo'aza ya ce, “A ranar da ka sayi gonar daga hannun Na'omi, sai kuma ka ɗauki Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayin, domin ka ta da zuriyar da za ta gaji marigayin.”

Rut 4