3. Sai ki yi wanka, ki shafa man ƙanshi, ki yafa tufafinki na ado, ki tafi masussukar, amma kada ki bari ya san zuwanki, sai bayan da ya riga ya ci ya sha.
4. Sa'ad da ya kwanta, sai ki lura da inda ya kwanta, sa'an nan ki tafi, ki buɗe mayafinsa a wajen ƙafafunsa, ki kwanta a ciki. Zai kuwa faɗa miki abin da za ki yi.”
5. Rut ta amsa, “Zan yi dukan abin da kika faɗa.”
6. Rut kuwa ta gangara zuwa masussukar, ta yi yadda surukarta ta faɗa mata.
7. Sa'ad da Bo'aza ya ci ya sha yana cikin jin daɗi, sai ya je ya kwanta kusa da tsibin tsabar sha'ir. Sa'an nan Rut ta tafi a hankali, ta buɗe mayafin da ya rufa da shi wajen ƙafafunsa, ta kwanta a ciki.
8. Da tsakar dare, sai mutumin ya farka a firgice, ya juya, sai ga mace kwance a wajen ƙafafunsa.