2. Sunan mutumin, Elimelek, matarsa kuwa Na'omi, 'ya'yanta maza kuma Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Baitalami ta Yahudiya. Suka tafi Mowab suka zauna a can.
3. Elimelek, mijin Na'omi, ya rasu, aka bar Na'omi da 'ya'yansu maza biyu.
4. Sai suka auri 'yan matan Mowab, Orfa da Rut. Bayan da suka yi wajen shekara goma a can,
5. sai kuma Malon da Kiliyon suka rasu, Na'omi kuwa ta rasa mijinta da kuma 'ya'yanta maza biyu.
6. Daga can Mowab, Na'omi ta ji cewa, Ubangiji ya taimaki mutanensa, ya ba su abinci, sai ta tashi daga ƙasar Mowab tare da surukanta.
7. Suka kama hanya zuwa ƙasar Yahudiya.
8. Amma a hanya, sai Na'omi ta ce wa surukanta, “Bari ko waccenku ta koma gidan iyayenta. Ubangiji ya yi muku alheri kamar yadda kuka yi mini alheri, ni da marigayan.