6. Amma a yanzu mun 'yantu daga Shari'a, mun mutu daga abin da dā ya ɗaure mu ke nan, har muna iya bauta wa Allah da sabon rai da Ruhu, ba da tsofaffin rubutattun ka'idodi ba.
7. To, me kuma za mu ce? Shari'a zunubi ce? A'a, ko kusa! Amma kuwa duk da haka, da ba domin Shari'a ba, da ban san zunubi ba. Da ba domin Shari'a ta ce, “Kada ka yi ƙyashi” ba, da ban san ƙyashi ba.
8. Amma zunubi, da ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya haddasa ƙyashi iri iri a zuciyata. Gama da ba domin shari'a ba, da zunubi ba shi da wani tasiri.
9. Dā kam, sa'ad da ban san shari'a ba, ni rayayye ne, amma da na san umarnin, sai zunubi ya rayu, ni kuma sai na mutu.
10. Umarnin nan kuwa, wanda manufarsa a gare ni rai ne, sai ya jawo mini mutuwa.
11. Don kuwa zunubi ya sami ƙofa ta hanyar umarni, sai ya yaudare ni, ta wurinsa kuwa ya kashe ni.
12. Domin haka Shari'a da kanta mai tsarki ce, umarnin kuma mai tsarki ne, daidai ne, nagari ne.