19. Nagarin abin da nake niyya yi kuwa, ba shi nake yi ba, sai dai mugun abin da ba na niyya, shi nake aikatawa.
20. To, idan abin da ba na niyya shi nake yi, ashe kuwa, ba ni nake yinsa ba ke nan, zunubin da ya zaune mini ne.
21. Sai na ga, ashe, ya zama mini ka'ida, in na so yin abin da yake daidai, sai in ga mugunta tare da ni.
22. Ni kam, a birnin zuciyata, na amince da shari'ar Allah.
23. Amma ina ganin wata ka'ida dabam a gaɓoɓina, wadda take yaƙi da ka'idar da hankalina ya ɗauka, har tana mai da ni bawan ƙa'idar nan ta zunubi wadda take zaune a gaɓoɓina.
24. Kaitona! Wa zai cece ni daga jikin nan, wanda yake kai ni ga mutuwa?
25. Godiya tā tabbata ga Allah, akwai, ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu! Ashe kuwa, ni a kaina, da hankalina, hakika Shari'ar Allah nake bauta wa, amma da jikina ka'idar zunubi nake bauta wa.