1. To, me ke nan za mu ce a game da Ibrahim, kakan kakanninmu?
2. Gama in da Ibrahim ya sami kuɓuta ta aikinsa na lada, ashe kuwa, yana da abin yin taƙama ke nan, amma fa ba a gaban Allah ba.
3. To, me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi.”
4. Wanda yake aikin lada, ladarsa ba kyauta ba ce, sakamakon aikinsa ce.