6. Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, don su mahukunta ma'aikata ne na Allah, suna kuma yin wannan aiki a koyaushe.
7. Ku ba kowa hakkinsa, masu haraji, harajinsu, masu kuɗin fito, kuɗinsu na fito, waɗanda suka cancanci ladabi, ladabi, waɗanda suka cancanci girmamawa, girmamawa.
8. Kada hakkin kowa ya zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Shari'a ke nan.
9. Umarnan nan cewa, “kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi ƙyashi,” da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”