Rom 1:5-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ta wurinsa ne muka sami alheri da kuma manzanci, saboda sunansa dukan al'ummai su gaskata su yi biyayya,

6. a cikinsu kuma har da ku da kuke kirayayyun Yesu Almasihu.

7. Daga Bulus zuwa ga dukan ƙaunatattun Allah da kuke a Roma, tsarkaka kirayayyu.Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

8. Da farko dai ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Almasihu saboda ku duka, domin ana baza labarin bangaskiyarku a ko'ina a duniya.

9. Domin kuwa Allah, wanda nake bauta wa a ruhuna ta yin bisharar Ɗansa, shi ne mashaidina a kan yadda kullum ba na fasa ambatonku a cikin addu'ata,

10. ina addu'a, ko ta ƙaƙa, da yardar Allah, a yanzu kam, in sami arzikin zuwa wurinku.

11. Domin ina ɗokin ganinku, in ni'imta ku da wata baiwa ta ruhu, domin ku ƙarfafa.

12. Wato ni da ku, mu ƙarfafa juna ta bangaskiyarmu, tawa da taku.

13. Ina so ku sani 'yan'uwa, na sha ɗaura niyyar zuwa wurinku, ko da yake har yanzu ba a yardar mini ba, domin ku ma in sami amfani a gare ku, kamar yadda na samu a cikin al'ummai.

14. Akwai hakkin Helenawa, da na bare, da na masu ilimi, da na jahilai duka a kaina.

15. Saboda haka a gwargwadon iyawata, ina da himma ku ma in yi muku bisharar, ku da kuke a Roma.

16. Gama ba na jin kunyar bishara, domin ita ce ikon Allah mai kai kowane mai ba da gaskiya ga samun ceto, Yahudawa da fari, sa'an nan kuma al'ummai.

Rom 1