Neh 6:10-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sa'ad da na ziyarci Shemaiya ɗan Delaiya, wato jikan wanda aka hana shi fita, sai ya ce mini, “Bari mu tafi cikin Haikalin Allah, mu rufe ƙofofin Haikalin, gama suna zuwa su kashe ka, za su iya zuwa a wani dare su kashe ka.”

11. Sai na ce, “Mutum kamata ne, zai gudu? Mutum irina zai shiga Haikali don ya tsere? To, ba zan tafi ba.”

12. Na gane Allah bai aike shi wurina ba. Ya yi mini wannan magana domin Tobiya da Sanballat sun haɗa baki da shi.

13. Gama da wannan nufi ne suka haɗa baki, don in ji tsoro, in yi yadda suke so, in yi zunubi, da haka za su ba ni mugun suna, su yi mini ba'a.

14. “Ya Allahna, ka tuna da Tobiya da Sanballat bisa ga abubuwan nan da suka yi, da annabiya Nowadiya, da sauran annabawa waɗanda suka so su tsoratar da ni.”

Neh 6