1. “Ku ji abin da ni Ubangijinake cewa,Tashi ku gabatar da ƙararku agaban duwatsu,Ku bar tuddai su ji muryarku.
2. “Ku duwatsu da madawwaman tussanduniya,Ku ji tuhumar da Ubangiji yake yimuku.Gama Ubangiji, yana da maganagāba da mutanensa,Zai tuhumi Isra'ila.
3. “Ya ku jama'ata, me na yi muku?Wace irin fitina nake yi muku?Ku amsa mini!
4. Gama na fito da ku daga ƙasarMasar,Na fanshe ku daga gidan bauta.Na aika muku da Musa, da Haruna,da Maryamu.